Da sunann Allah mai rahama.

Koyi  da soyayyar Ubangiji da yaki da barna

Kissar  Annabi Ibrahim masoyin Allah.

وَتَاللَّهِ لَأَكِيدَنَّ أَصْنَامَكُم بَعْدَ أَن تُوَلُّوا مُدْبِرِينَ فَجَعَلَهُمْ جُذَاذًا إِلَّا كَبِيرًا لَّهُمْ لَعَلَّهُمْ إِلَيْهِ يَرْجِعُونَ 

Wallahi sai na yi wa gummakanku illa bayan kun juya baya .Sai ya maida su guntu-guntu sai babban su kawai wata kila ya basu labarin yadda aka yi idan sun dawo.Anbiya'a:57-58)

Bayanin kissar:

Annabi Ibrahim A.S. yana daya daga cikin manyan Annabawan Allah T.A da ya aiko zuwa ga bayinsa, Sannan ma shi ne na biyu daga cikin Annabawan da ake ce wa ulul azm.

Kissar Annabi Ibrahim tana daya daga  cikin kissoshi masu darasi da kawatarwa a cikin alkur'ani, wanda ayoyi da surori da dama suka zo da bayaninta ta siga daban-daban.

Labarin karya gumakan da Annabi Ibarahim ya yi yana daya daga cikin muhimmin wannan kissa.Annabi Ibrahim a.s. tun yana saurayi matashi ya  gabtar da wannan aiki muhimmi na karya gumaka da kuma tattaunawa da ya yi da dan uwan babansa wato Azar dangane da bautar gumaka da kawo masa dalilai daya yi a kan rashin can-cantar gumaka wajen bauta.

 Kur'ni ya cigaba da bada kissar Ibrahim, inda ya yi amfani da kalmar Baba wajen dan uwan mahaifin annabi Ibarahim a.s. domin larabawa sukan yi amfani da kalmar Baba wajen dan uwan Uba. Don haka ne wadan su a nan sukan ce wai Azar Baban Annabi ibrahim ne alhalin kuwa ba mahaifinsa ba ne, wasu malam Tafsiri sun yi amfani da wannnan kalma ne Ta "ab" a matsayin Baba. Duk da yake bincike ya tabbadar da sabanin hakan. Wato cewa ba Mahaifinsa ba ne.

 Annabi Ibahim ya cigaba da cewa: Mene ne wadannan Gumaka   kuke mika wuyanku zuwa garesu dare da rana kuna zagaya su ba ku barin wannan aiki?

Annabi Ibarahim yin amafani da ya yi da kalmar Gunki a kan wadan alloli na sukamar ya   wulakanta su ne saboda tsananin girmansu da suke gani.saboda ya kamanta su da kamar wani abin wasa wato wani butum- butumi, yana so ya nuna musu cewa wadannan Gumaka ba wani abu ba ne face Butun-butumi wanda ba ya iya yi wa kansa komai balantana waninsa.

Wannam Magana ta Ibrahim babban dalili ne na rusa bautar gumaka, saboda gunki ba wani abu ba ne face butun-butumi, wane mutum ne da   hankalinsa zai ba shi dama ya je yana girmama irin wannan butun-butumi? Wanda ba komi ba ne sai yankin dutse da itaciya. Wanda mutum mai daraja irin wannan ya zai je yana bautawa abin da ya sassaka da hannunsa har ya nemi biyan bukatarsa daga garesa?

 Amma lokacin da Baban annabi Ibarahim da wadan da suke tare suka rasa amsar da zasu ba shi sai suka ba shi amsa marar ma''ana suka ce: wannan abin ne iyayenmu da kakanninmu suka yi, haka neb a mud a dalili akan hakan amma tabbas iyayenmu sun fi mu sani, don haka suna da dalili, saboda haka muma ba zamu bar abin da muka samu iyayenmu da kakanni suke yi ba.

 Amma kasancewar kawai mun samu iyayenmu suna yin wani aiki ba dalili bane da zai tabbatar da gaskiya abin, sannan ba dalili ba ne da ke nuna cewa sun fi mu sani kuma sun fi mu hankali. Domin babu wani dalili dake nuna cewa mutanen baya sun fi na gaba hankali.

 Annabi Ibrahim ba tre da bata lokaci ba sai ya ba su amsa da cewa:Ku da Iyayenku tabbas kun kasance cikin bata a bayya ne.Wannan amsa ta sa fa, tasa masu bautar gumaka baki daya su maido hankalinsu da kyau wajensa, shi ya sa fa sai gaba daya suka kallo shi, suka ce: shin wai da gaske kake ko kuwa kana wasa ne?

  Sai Ibrahim a.s shima fa sai ya basu amsa da cewa: Abin da fa nake fada da gaske nake kuma shi ne hakika, kuma Ubangijinku shi ne Ubangijin sammai da kassai.wanda shi ne Allah wanda ya halicce su kuma ni na yi Imani da hakan. Annabin domin ya tabbatar musu da gaskiyar abin da yake fada kuma ya nuna musu gaskiyar imaninsa akan abin, dari bisa dari kuma a shirye ya ke da duk abin da zai bi yo baya  sai ya ce:

 Ina rantsuwa da Allah sai na gama da gumakanku bayan baku nan. Daga nan fa suka fahimci cewa lallai Ibrahim sai ya gama da Gumakansu. Daga nan fa Ibrahim ya kasance kawai yana neman dama ne don ya aikata abin da ya yi alkawali.

Masu bautar Gumakan suna da wata al'ada kowace shekara suna yin bikin edi wato sai kowa ya yi abinci daga gidansa sai su kawo wajen bautarsu,sai su hadu wuri guda su fita wajen gari sai rana faduwa zasu dawo, sannan sai su zo su ci abinci da ma'nar wai gumakan sun sa musu albarka.Don haka wannan rana sai suka nemi Annabi Ibrahim da shima ya zo su tafi wajen wannan al'ada da suke yi ko wace shekara, amma sai ya nemi uzri da cewa ba ya lafiya saboda haka sai bai bi su ba. Annabin ya samu damar da yake nema fa, ba tare da wani shakku ba akan a bin da zai iya biyo baya, cikin gwarzantaka ya ta shi fa ya tari wannan al'amari mai girman gaske wanda fada  ne da dukkan mutanensa. Kamar yadda Kur'ani maigirma yake fada ya yi musu guntu-guntu sai babban su kawai ya dora Gatarin a kafadarsa ko ya ba su labarin abin da ya faru, kamar yadda aya ta farko da muka kawo take bayanin hakan.

 Daga karshe dai sai rana ta fadi suka dawo kamar yadda suke yi domin su kai gaisuwa zuwa ga Gumakansu, kuma su ci abincin da suka bari don a sa musu albarka. Lokacin da fa suka shiga wajen bautar sai kau suka ga abin da ya firgita su. Wanda sun bar gidan bautarsu cikin kayatarwa sun da wo sun sami duk gumakansu a karye. Sai su ka yi tsawa da karfi suna cewa: wa ya yi wannan mummunan aiki, tabbas duk wanda ya yi wannan aiki azzalumi ne, lallai ya zalunci allolinmu kuma ya zalunci kasa da al'umma baki daya, kuma lallai ya aikata abin da zai hallakar da shi.

 Amma wadansu da ba su manta ba da  maganar da Ibarahim ya yi akan Gumakan  nasu na wulakacin da cin mutunci, sai suka ce: Mun ji wani yaro a na ce ma sa Ibarahim yana maganganun batanci akan su. Sai manya-manya su suka ce a yi shela duk wanda ya ji Ibrahim na yin irin wannan maganganun ya zo ya ba sheda

Da sauri wadan da suke da masaniya akan hakan suka hallara, sannan kuma mutane da yawa suka hallara don su ga me zai faru a kansa. Abu fa  ya yadu cikn gari da ban al'ajabi domin wani abu makamancin wannan bai taba faruwa ba, duk fa suka hadu don kallo.

 Sai kau aka halarto da Ibarahim aka tambaye shi, cewa: kai ne ka aikata wannan aiki ga allolinmu Ibrahim? Sai ya ce: ku tambayi babbansu ga shi nan idan sun kasance suna magana. Sai kowa ya dubi dan uwansa fa suka soke kai a kasa. Sai suka ce ai kasan ba sa magana Ibarahin. Sai ya ce yanzu zaku bauta wa wanin Allah wanda ba ya yi muku amfanin komi kuma ba ya iya cutar da ku? Ku kam kaiconku da abin da kuke bautama wa ba Allah ba, me ya sa ba ku da hankali? Sai fa suka fusata suka ce ku kona shi idan kuna iya taimakon allolinku.

 Sai fa kafirai makiya Allah da gaskiya suka hada wuta domin su kona Ibrahim sakamakon abin da ya yi musu na gamawa da allolinsu. Suka hadu akan haka suka jefa Annabin Allah a cikin wuta, Sai kau Allah mai kowa da komi ya Umurci wuta da kada ta kona Annabin Allah ibrahim, sai wuta ta koma mai sanyi na aminci da jin dadi a garesa.

 Wadannan ma'abota gumaka sun yi nufi sharri ga Annabin Allah sai Allah ya maida musu mafi sharrinsu, kuma ya tseratar da Annabinsa. Allah madaukaki ya cigaba da cewa: sai muka tseratar da shi da Annabi Lud zuwa kasar da muka sa mata albarka ga halitta. Kuma muka ba shi da Ishaka da Ya'akub, sannan kuma muka sa su salihan bayi.

 Wannan ita ce Kissar Annabin Allah Ibrahim a.s wadda take koyar da mu tsananin son Allah da dagewa akan hanyarsa, komin wuya komin dadi ba tare da ja da baya ba. Sannan tana nuna mana yadda idan mutum ya tsaya a kan gaskiya lallai shi ne zai yi nasara. Sannan mutumin da ya dage akan bata lallai karshensa tabewa ce.

 Da fatan Allah ya nuna mana gaskiya ya kuma ba mu ikon binta har karshen rayuwarmu amin.