Ubangiji Madaukakin Sarki (S.W.T)

Mun yi imani cewa Allah Madaukaki daya ne makadaici babu wani abu kamarsa, wanzazze bai gushe ba kuma ba ya gushewa, Shi ne na farko kuma Shi ne na karshe, Masani, Mai Hikima, Adali, Rayayye, Mai Iko, Mawadaci, Mai ji, Mai gani. Ba a siffanta Shi da abinda ake siffanta halittu, shi ba jiki ba ne, kuma ba sura ba ne, ba jauhar[i] ba ne kuma ba ard[ii] ba ne, ba Shi da nauyi ko sakwaikwaya, ba Shi da motsi ko rashin motsi, ba Shi da guri ba Shi da zamani kuma ba a nuni zuwa gare Shi, kamar yadda babu kini gare Shi, babu kama, babu kishiya, babu mata gare Shi, babu abokin tarayya, kuma babu wani tamka gare Shi.

Maganai ba sa riskar Sa Shi kuwa yana riskar maganai, duk wanda ya ce ana kamanta Shi to ya zamar da Shi halitta ke nan, wato ya suranta fuska gare Shi da hannu da kuma idaniya, (kuma cewa Shi yana saukowa zuwa saman duniya, ko kuma cewa zai bayyana ga 'yan aljanna kamar wata ko kuma makamantan wannan, to lalle yana matsayin wanda ya kafirce da Shi ne wanda ya jahilci hakikanin mahaliccin da ya tsarkaka daga nakasa, kai dukkan abinda muka bambance Shi da sake-saken zukatanmu a mafi daldalewar ma'anarsa to Shi abin halitta ne kamarmu mai komawa ne gare mu kamar yadda Imam Bakir (A.S.) ya fassara shi gare mu da bayani mai hikima da kuma zurfin ma’ana ta ilimi mai zurfi.

Har ila yau ana kirga duk wanda ya ce yana nuna kansa ga halittunsa ranar Kiyama a cikin kafirai[iii] koda kuwa ya kore masa kamantawa da jiki, batun baka ne kawai kuma irin wadannan masu da'awa sun sandare ne kawai a kan wasu laffuza na zahiri na Alkur'ani ne ko wasu hadisai kuma suka karyata hankulansu suka yi watsi da su. Don haka suka gaza yin aiki da zahiri gwargwadon yadda nazari da dalilai suka hukunta da kuma ka'idojin lakabi da kuma aron ma'anar kalma.

Tauhidi (Kadaita Allah)

Mun yi imani ya wajaba a kadaita Allah ta kowace nahiya, kamar yadda ya wajaba a kadaita shi a zatinSa haka nan muka yi imani da cewa Shi kadai ne a zatinsa da wajabcin samuwarSa, kazalika ya wajaba kadaita Shi a siffofi. Wannan kuwa saboda imani ne da cewa siffofinSa ainihin zatinsa ne kuma Shi a ilimi da kudura ba Shi da na biyu a halitta da arzutawa kuma ba Shi da abokin tarayya, a cikin dukan kamala kuma ba Shi da kwatankwaci.

Haka nan mun yi imani da kadaita Shi a bauta bai halatta a bauta wa waninsa ba ko ta wace fuska, kamar kuma yadda bai halatta ba a hada Shi da wani abu nau’in nauo'in ibada, wajiba ce ko kuma wadda ba wajiba ba, a salla ne ko kuma a wasu da ba ita ba na daga ibadoji.

Duk wanda ya yi shirka ya hada wani da Shi a ibada to Shi Mushiriki ne kamar kuma wanda yake riya a ibadarsa yana neman kusacin wanin Allah (S.W.T), hukuncinsa Shi wanda ya yi haka hukuncin wanda ya bauta wa gumaka ne babu bambanci a tsakaninsu.

Amma abinda ya shafi ziyartar kaburbura da kuma gudanar da bukukuwa ba sa daga cikin nau'in neman kusaci ga wanin Allah ko ibada kamar yadda wasu daga masu son suka ga tafarkin Shi'a Imamiyya suke so su raya suna masu jahiltar hakikanin al'amarin, Sai dai wannan wani nau'i ne na kusanci ga Allah (S.W.T) ta hanyar kyawawan ayyuka, kamar neman kusaci gare Shi ta hanyar gaishe da marar lafiya, da raka gawa zuwa kabari, da ziyartar 'yan'uwa a Addini, da kuma taimakon fakiri.

Don zuwa gaishe da marar lafiya Shi a kan kansa alal misali, kyakkyawan aiki ne wanda mutum kan samu kusaci ga Allah ta hanyarsa, ba neman kusaci ga marar lafiyar ba ne da zai zamar da aikata Shi ya zama bauta ga wanin Allah (S.W.T) ko kuma shirka a bautarSa.

Haka nan sauran misalan kyawawan ayyuka irin wadannan wadanda a cikinsu har da ziyartar kaburbura, da gudanar da bukukuwa, da rakiyar gawa zuwa kabari da kuma ziyartar 'yan'uwa. Amma kasancewar ziyartar kaburbura da bukukuwan Addini a matsayin kyawawan ayyuka a shari'a al'amari ne da fannin fikihu ke tabbatar da Shi ba nan ne gurin tabbatar da Shi ba.

Manufa ita ce cewa aikata irin wadannan ayyukan ba sa daga cikin shirka a ibada kamar yadda wasu suke rayawa kuma ba ma ana nufin bauta wa Imamai da su ba ne, abin nufi da su kawai Shi ne raya al'amarinsu, da kuma sabunta tunawa da su, da kuma girmama alamomin Addinin Allah da tare da su "wannan, duk wanda Ya girmama alamomin Addinin Allah to lalle wannan yana daga cikin ayyukan ibadar zukata." Surar Hajj.

Siffofin Ubangiji (S.W.T)

Mun yi imani cewa daga cikin siffofinsa akwai wajiban siffofi tabbatattu na Hakikanin kamala da ake kira siffofin jamal da kamal, wato kyawu da kamala, kamar ilimi da iko, da wadata, da irada, nufi, da rayuwa wadanda su kansu su ne ainihin zatinSa, su ba siffofi ba ne da su ke kari a kan zatinSa. Ainihin samuwarsa ba wani abu ba ne a kan zatinsa, kudurarsa kuma dangane da rayuwarsa, rayuwarsa ita ce kudurarsa, Shi mai kudura ne ta yadda yake rayayye, kuma rayayye ta yadda yake mai kudura, babu tagwaye tsakanin siffofinSa da samuwarsa, haka nan kuma a sauran siffofinsa na kamala.

Na'am siffofinsa sun sha bamban a ma'anoninsu da manufofinsu amma ba wai a hakikaninsu da samuwarsu ba saboda idan da sun kasance haka to da lalle ya kasance an sami wajibabbun samammu da dama kuma da ba a sami kadaitaka ta hakika ba wannan kuwa ya saba wa Akidar Tauhidi.

Tabbatattun siffofi kamarsu halitta da arzutawa kuwa, da gabatarwa, da kuma musabbabi duk alal hakika suna komawa ne ga siffa guda ta hakika, ita ce kasancewarsa mai tafiyar da al’amauran bayinsa, wannan ita ce siffa guda wadda siffofi da dama ke samuwa daga gare ta gwargwadon tasirori dabam-daban da kuma la'akari iri daban daban.

Amma siffofin da ake kira salbiyya wato korarru wadanda kuma ake kiran su siffofin Jalala, siffofin girma, su dukansu suna komawa ne ga siffa korarriya guda, wanda ita ce siffar kore kasancewarsa mai yiwuwar samuwa ba wajibin samuwa ba, ma'anarsa kore jiki gare Shi, da kore sura, da kore motsi, da kore­ rashin harka, da kore nauyi, da kore rashin nauyi, da dai sauran makamantansu, wato dai kore dukkan nakasa.

Sa'an nan kuma kore kasancewarsa ba wajibin samuwa ba yana tabbatar da kasancewarsa wajibin samuwa, wajabcin samuwa kuwa na daga cikin siffofi tabbatattu na kamala, don haka siffofin Jalala korarru a karshe suna komawa ne ga siffofin kamala tabbatattu, Allah (S.W.T) kuwa Shi kadai ne Makadaici ta kowace fuska, babu adadin yawantaka a zatinSa, babu kuma muhawara a hakikaninsa makadaici abin nufi da bukata.

Abin mamaki ba zai kare ba ga maganar wanda yake da ra'ayin cewa siffofin tabbatarwa wadanda suke wajibai ga Allah duk suna komawa ne ga siffofin da suke korarru, Sai ya yi masa wahala ya fahimci cewa siffofinSa su ne ainihin zatinSa, don haka sai ya kintata cewa siffofin subutiyya tabbatattu wajibai ba sa koruwa ga Allah duk suna komawa ga korarrun siffofi ne domin kawai ya natsu da fadin kadaitaikar zati da rashin yawaitarsa sai kawai ya auka a cikin abinda ya fi shi muni domin zamar da ainihin zati (wanda shi ne samuwa, tsantsan samuwa wanda ba shi da duk wata nakasa da kore duk wata mafuskanta da ba ta dace da wanda yake  wajibin samuwa ba) ya sanya shi ya zama aininin rashi kuma ainihin korarre. Allah ya kiyayye mu daga tabewar wahamce-wahamce da kuma tuntuben duga-dugai.

Kamar yadda mamaki ba zai kare ba ga wanda ke da ra'ayin cewa siffofinSa na subutiyya, tabbatattu, kari ne a kan zatinSa, saboda haka wanzazzu suna da dama kenan, ya kuma wajabta abokan tarayya ke nan ga wajibin samuwa Ubangiji madaukaki ya kuma sanya shi mai hauhawa daga gabbai.

Sayyyidina Ali Amirul Muminin (A.S.) kuwa ya ce:

Cikar Ikhlasi gare shi kuwa Shi ne kore siffofi gare Shi (wato siffofn kari da na khabariyya wadanda ake tawilinsu kamar tawilin hannu da karfi ko iko ko alkawarin Allah kamar yadda ya zo da kinayoyi da kalmomin aro a Alkur'ani mai girma) saboda shaidar cewa dukan abin siffantawa to ba shi ne siffar ba, da kuma shaidar cewa dukan abin siffantawa ba shi ne siffar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah  (da irin wadancan siffofi) to ya gwama shi wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita shi wanda ya tagwaita Shi kuwa ya zamar da Shi sassa­-sassa, wanda sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi."

Adalcn Allah

Adalci yana daga cikin siffofin Allah (S.W.T) Assubutiyya kamaliyya wato tabbatattun siffofin kamala akwai cewa shi adali ne ba azzalumi ba, ba ya karkacewa a hukuncinsa ba ya tabewa a hukuncinsa, zai yi sakayya ga masu biyayya kuma yana lalle shi zai hukunta masu sabo ba ya kallafawa bayinsa abinda ba za su iya ba ba zai musu ukuba fiye da abinda suka cancanta ba kuma mun yi imani cewa Ubangiji ba ya barin abu mai kyau matukar ba wani abin da zai hana aikata shi, yana yin  abu wanda shi ne mai kyau kuma ba ya aikata mummuna saboda Shi Ubangiji mai kudura ne a kan ya aikata kyakkyawa ya bar mummuna tare da cewa yana da sani  game da kyawun kyakkyawa da kuma munin mummuna da wadatuwarSa ga barin kyakkyawan da kuma aikata mummunan, babu wani kyakkyawan (aiki) da aikata shi zai cutar da Shi, babu kuma wani mugun aiki da yake bukatarsa ballantana ya aikata shi kuma duk da haka mai hikima ne babu makawa aikinsa ya kasance ya dace da hikima kuma daidai gwargwadon tsari mafi kamala Idan har da zai aikata zalunci da kuma mummunan aiki to da al'amarin hakan ba zai rabu da daya daga cikin surorin nan hudu:

 1- Ya kasance ya jahilci al'amarin bai san cewa mummuna ba ne.

2- Ko kuma ya kasance yana san da shi amma kuma ya aikata shi ala tilas ya gaza barin aikata shi.

3- Ko kuma ya kasance yana sane da shi ba a kuma tilasta shi ya aikata ba bai kuma gaza kin bari ba amma yana bukatar aikatawa.

4- Ko kuma ya kasance yana sane da shi, ba mai aikata shi ala tilas ba, ba kuma mai bukata ya zama ya takaita ke nan da aikata shi a bisa Sha'awa da wasa da bata lokaci.

Dukan wadannan sun koru ga Allah domin suna tabbatar da nakasa gare shi alhali Shi kuwa zallan kamala ne saboda haka wajibi ne mu hukunta cewa shi tsarkakakke ne daga zalunci da kuma aikata abinda yake mummuna.

Sai dai kuma wani bangare daga cikin musulmi sun halatta wa Allah (S.W.T) aikata mummuna (Sunayensa sun Tsarkaka) suka halatta cewa zai iya azabtar da masu biyayya, ya kuma shigar da masu sabo aljanna kai hatta kafirai ma kuma suka halatta cewa yana iya kallafa wa bayinsa abinda ya fi karfinsu da abinda ba za su iya aikatawa ba  amma kuma duk da haka ya azabtar da su idan har suka bari ba su aikata shi ba. Har ila yau kuma sun halatta zalunci na iya faruwa daga gare Shi da tabewa, da karya da yaudara, kuma ya aikata aiki ba tare da wata hikima ba, ba da manufa ba, ba da amfani ba, ba da fa'ida ba, da hujjar cewa;

"Ba a tambayar sa a kan abinda yake aikatawa su kuwa ana tambayar su." Surar Anbiya: 23.

Da yawa daga cikin irin wadannan da suka suranta Shi a kan wannan Akida tasu batacciya da cewa Shi, Azzalumi ne, mai Ja'irci, mai wauta ne, mai wasa ne, mai karya ne, mai yaudara ne, yana aikata mummuna, yana kuma barin kyakkyawa,(Allah  ya daukaka ga aikata wadannan abubuwa, daukaka mai girma,) wannan shi ne kafirci tsantsansa.

Kuma Allah Ta'ala Ya ce:

"Kuma Allah ba ya nufin zalunci ga bayi." Surar Mumin ayata 23.

"Kuma Allah  ba ya son barna." Surar Bakara: 31

"Kuma ba mu halitta sammai da kasa da abinda ke tsakaninsu muna Masu wasa ba." Surar Dukhan: 205.

"Kuma ban halitta Aljannu da Mutane ba face don su bauta mini." Surar Zariyat: 56.

Wajabta Aiki.

Mun yi imani cewa Allah (S.W.T) ba ya kallafa wa bayinsa aiki sai bayan ya tabbatar musu hujja a kansu kuma ba ya kallafa musu sai abinda za su iya aikata shi kuma suke da ikon aikata shi kuma suka san shi domin yana daga zalunci kallafa aiki ga ajizi, wanda ba zai iya ba, da kuma Jahilin wanda ilimi bai isa zuwa gare shi ba, ba wai ya ki neman ilimin da ganganci ba.

Amma shi kuwa Jahili wanda ya ki neman sani da gangan alhali yana da damar samun ilimin hukunce-hukunce da ayyukan ibada to shi ne mai amsa tambaya a gurin Allah ne kuma shi za a yiwa ukuba a kan sakacinsa domin wajibi ne a kan kowane mutum ya koyi abinda yake bukata na daga hukunce-hukuncen shari'a. Kuma mun yi imani cewa: Allah (S.W.T) babu makawa Ya kallafa wa bayinsa ayyuka ya kuma sanya musu shari'o'i abinda na amfani da kuma alheri gare su a cikinta domin ya sanya su a kan hanyoyin alheri da rabauta dindindin, sa'an nan kuma ya shirye su zuwa ga abinda yake shi ne maslaha kuma ya gargade su game da abinda yake akwai fasadi da barna a cikinsa da kuma cutarwa gare su, da kuma mummunan karshe gare su, ko da kuwa ya san cewa su ba za su bi Shi ba, domin wannan tausasawa ne da kuma rahama ga bayinSa don kasancewarsu sun jahilci mafi yawancin amfanin kansu da hanyoyinsu a nan duniya da kuma lahira. Sun jahilci da yawan abubuwan da za su jawo musu cuta da hasara, Shi kuwa Ubangiji Shi ne Mai Rahama mai Jin kai a ainihin zatinSa, Shi kamala ne tsantsa wanda kuma shi ne ainihin zatinSa kuma har abada bai rabu daga gare shi.

Wannan tausasawa kuwa ba za ta gushe ba, don bayinsa sun kasance sun bijire sun ki bin sa, sun ki kayyaduwa da umarce-umarcensa kuma sun ki hanuwa da hane-hanenSa.

Kaddara

Jama'ar Mujabbira (masu ganin aikin bawa aiki ne na Ubangijinsa) sun tafi a kan cewa Allah (S.W.T) mai aikata ayyukan halittu don haka sai ya zamanto ke nan ya tilasta mutane a kan aikata sabo duk da haka kuma ya yi musu azaba, Sa'an nan kuma ya tilasta su a kan abinda ya yi umarni, duk da haka kuma ya ba su lada domin sun tafi akan cewa lalle ayyukansu tabbas ayyukanSa ne, ana dai danganta ayyukan su ne kawai a garesu domin musamaha domin su ne mahallan ayyukan na Ubangiji. Asalin wannan kuwa shi ne kasancewar su sun yi inkarin musabbabai na dabi'a a tsakanin abubuwa domin sun yi tsammani cewa hakan shi ne ma'anar kasancewar Ubangiji mahalicci, da ba Shi da abokin tarayya kuma Shi ne mai sabbabawa na ainihi ba waninSa ba. Duk wanda yake fadin irin wannan ra’ayi kuwa hakika ya danganta zalunci ga Allah Shi kuwa ya daukaka ga haka.

Wasu jama'a kuma wato Mufawwadha sun yi imanin cewa Allah ya sallama ayyuka ne ga halittu, ya janye kudurarsa da hukuncinsa da kuma kaddarawarsa daga gare su, wato danganta ayyuka gare shi yana nufin dangata nakasa gare shi, kuma samammun halittu suna da nasu musabbaban na musamman koda yake dai dukansu suna komawa ne ga musabbabi guda daya na farko wanda shi ne Allah (S.W.T).

Duk wanda yake fadin wadannan irin maganganu to lalle Ya fitar da Allah  daga mulkinSa ya kuma yi shirka da shi da halittunSa.

Kuma mun yi Imani muna masu biyayya ga abinda ya zo daga lmamanmu tsarkakakku da ke cewa al'amari ne tsakanin al'amura biyu (kuma tafarki matsakaici a tsakanin maganganun biyu) wanda irin wadannan ma'abota tsaurin kan suka gaza fahimtarsa wasu suka zurfafa wasu kuma suka yi takaita, babu wani daga cikin masana ilimi da ma'abuta falsafa da ya fahimce shi sai bayan karnoni.

Ba abin mamaki ba ne ga wanda ba shi da masaniya game da hikimar Imamai (A.S.) dangane da al'amari tsakanin al'amura biyu ba, da kuma hanya matsakaiciya ba a maganganun biyu ya ce wannan batu ne daga cikin al'amuran da masana falsafa a Yammacin Turai na baya bayan nan suka gano alhali kuwa Imamai sun riga su tun kafin karni goma da suk wuce. Imam Sadik (A.S.) yayin da yake bayanin hanyar nan matsakaiciya yana cewa: "Babu Jabru, (Tilastawa) kuma babu sallamawa ayyuka baki daya sai dai al'amari ne tsakanin al'amuran guda biyu.

Wannan ma'ana girmanta na da yawa manufarta kuma na da zurfi, abin nuni a takaice shi ne cewa: Hakika ayyukanmu a bangare guda ayyukanmu ne alal hakika kuma mu ne musabbabansu na dabi'a kuma suna karkashin ikonmu da iyawarmu, a daya bangaren kuma su ayyukan kudurar Allah ne kuma suna cikin karkashin ikonsa domin Shi ne mai ba da samuwa mai samar da ita, bai tilasta mu a kan ayyuka ba ballantana ya zama ya zalunce mu a kan yi mana ukuba idan har muka saba, Saboda muna da iko da kuma zabi a kan abinda muke aikatawa. Kuma bai sallama mana samar da ayyukanmu ba ballantana ya zamanto ya fitar da su daga karkashin ikonsa ba, Shi dai Shi ne Mai halittawa Shi ne kuma mai hukuntawa, Shi ne kuma mai umarni, Shi kuma Mai iko ne a kan kome, kuma a kewaye yake da bayinsa.

Ko ta halin kaka dai abinda muka yi imani da shi game da hukuncin Allah da kuma kaddara shi ne cewa sirri ne daga asirran Allah (S.W.T) duk wanda ya iya ya fahince shi yadda ya dace ba tare da kwauro ko zurfafawa ba to shi kenan, idan kuwa ba haka ba to ba wajibi ba ne Ya kallafa kansa cewa sai ya fahimce shi daidai wa daidai, domin kada ya je ya bata Akidarsa, kuma ta baci saboda wannan yana daga cikin al'amura masu wahala, har ma sun fi binciken al'amuran falsafa zurfi da babu mai iya gane su sai 'yan kalilan daga cikin mutane wannan shi abinda ya sa da yawa daga cikin ma'abuta ilimin akida suka tabe.

Don haka kallafa shi ma ga bayi kallafa abu ne da ya fi karfin mutum wanda yake daidai da sauran mutane. ya wadatar mutum ya yi Imani da shi a dunkule kawai yana mai biyayya ga maganar Imamai tsarkaka amincin Allah ya tabbata gare su cewa shi wani al'amari ne tsakanin al'amura guda biyu, babu tilastawa babu kuma sallamawa a cikinsa. Kuma shi baya daga cikin jigo daga jiga-jigan Addini ballantana ya zama kudurcewa da shi wajibi ko ta halin kaka filla-filla daram.

Bada

"Bada" ga mutum: Shi ne wani sabon ra'ayi ya bayyana gare shi wanda a da can bai kasance yana da wannan ra'ayin ba, wato ya canja himmarsa da ya yi a kan wani aiki da ya kasance yana nufin aikata shi, wannan kuma saboda Jahilci ne game da amfani da kuma nadama a kan abinda ya riga ya gabata daga gare shi.

"Bada" da wannan ma'anar ya koru ga Allah (S.W.T) domin kuwa yana daga jahilci ne da nakasa wannan kuwa ya koru ga Ubangiji Shi'a Imamiyya kuma ba su yarda da shi ba.

Imam Sadik Alaihis Salam Ya ce:

"Wanda Ya yi da'awar cewa Canji cikin wani abu ya auku ga Allah (S.W.T) game da wani abu canji irin na nadama to agurinmu wannan Kafiri ne a game da Allah mai girma. Har ila yau kuma Ya ce: "Wanda ya raya cewa wani abu na Canjin ra’ayi ya faru ga Allah wanda da ya kasance bai san shi ba jiya to ni ba ni ba shi''.

Sai dai kuma akwai wasu Hadisai da aka ruwaito daga Imamanmu wadanda suke kamar nuni da ma'anar "Bada" yadda ta gabata kamar yadda ya zo daga Imam Sadik (A.S) cewa: "Bada bai taba yiwuwa ga Allah ba kamar yadda ya yiwu gare shi ba a kan Isma'ila dana.

Don haka ne wadansu marubuta daga cikin bangarorin musulmi suka dangata Bada ga Shi'a Imamiyya don yin suka ga mazhaba da tafarkin Ahlul Bait (AS) suka sanya shi ya zama abin kyama ga Shi'a. Sahihin al'amari a nan shi ne mu fadi kamar yadda Ya fada a Alkur'ani:

 "Allah yana shafe abinda ya so kuma yana tabbarwa Asalin littafi kuma gare Shi yake." Surar Ra'ad: 39.

Abin nufi shi ne cewa Allah (S.W.T) na iya bayyana wani abu a bisa harshen Annabinsa ko waliyinSa ko kuma a zahiri wata maslaha ta sa bayyanawar sa'an nan daga baya kuma ya shafe shi ya zama ba abinda ya bayyana da farko ba, kamar yadda ya faru a kissar Annabi Isma'il (A.S.) yayin da mahaifinsa Annabi Ibrahim (A.S.) Ya ga yana yanka dan shi a mafarki.

Wato kenan ma'anar maganar Imam (A.S) sai ta zama kenan cewa: Babu wani abu da ya bayyana ga Allah (S.W.T) na daga al'amari a kan wani abu kamar yadda ya bayyana gare shi a kan Isma'ila dansa domin (Allah) ya dauke shi (Isma'ila) Kafin shi (Imam Sadik (A.S.) domin mutane su san, (cewa) shi (Isma'ila) ba Imami ba ne, bayan a zahiri ya riga ya bayyana cewa shi ne Imami bayansa saboda shi ne babban dansa.

Abu da yake da "Bada" a ma'ana kuma shi ne shafe hukunce-hukuncen shari'o'in da suka gabata da shari'ar Annabinmu Muhammadu (S.A.W) hatta ma shafe wasu daga cikin hukunce-hukuncen shi Annabin namu (S.A.W).

Hukunce-hukuncen Addini

Mun yi imani cewa Ubangiji ya sanya hukunce-hukunce wajibai da haram da sauransu daidai da maslaha da alheri ga bayinSa a cikin ayyukan, abinda maslaharsa ta zama babu makawa ya sanya shi wajibi, wanda kuma cutarwar da ke tare da shi ta kai matuka sai ya haramta shi, wanda kuwa maslaharsa ta zama da kadan ta rinjayi cutarwarsa ya sanya mana shi mustahabi.

Haka nan sauran hukunce-hukuncen, wannan kuwa yana daga adalcinsa da kuma tausasawarsa ga bayinsa kuma babu makawa ya zamanto yana da hukunci a kan kowane al'amari, babu wani abu daga cikin abubuwa da zai zamanto ba shi da hakikanin hukuncin Allah a kansa koda kuwa tafarkin saninsa a toshe yake gare mu. Kuma har ila yau muna cewa yana daga mummunan abu ya zamanto ya yi umarni da aikata abinda yake akwai cutarwa a cikinsa, ko kuma ya hana abinda akwai maslaha a cikinsa.

Wasu daga cikin bangarorin musulmi suna cewa mummunan abu shi ne kawai abinda Ubangiji ya hana, kyakkyawa kuwa shi ne abinda ya kyautata kuma ya yi umarnin aikatawa, ba wai ainihin maslaha da cutarwar a ayyukan suke ba, kuma babu kyawu ko rashin kyawu a cikin ayyukan, Wannan magana kuwa ta saba wa abinda hankali yake hukuntawa.

Kazalizaka sun halatta cewa Allah na iya aikata mummuna ya yi umarni da abu wanda akwai cutarwa a cikinsa kuma ya hana abinda yake akwai maslaha a cikinsa.ya riga ya gabata cewa wannan irin magana akwai rashin girmamawa a cikinta kwarai. Saboda wannan magana na hukunta danganta jahilci da gazawa ga Allah, (Allah ta’ala Ya daukaka, daukaka mai girma ga barin irin wadannan siffofi).

A takaice dai abinda yake sahihi a Akida shi ne, mu ce: Shi Allah T'a'ala ba Shi da wata maslaha ko fa'ida a kallafa wajibai da kuma haramta haramtattu, maslahar da fa'idojin duka suna komawa ne gare mu a dukan ayyuka, Kuma babu wata ma'ana wajen a kore maslaha ko barna game da ayyukan da aka yi umarni ko aka hana aikatawa. Allah ba ya umarni don wasa ba ya hani haka banza shi kuma mawadaci ne ga barin bukatar bayinsa.


[i]- Abinda yake bai damfara ko dogara da wuri ba.

[ii] - Abinda yake ya damfara ko ya dogara da wuri.

[iii] - karfici a nan ba irin wanda yake fitar da mutum daga Musulunci ba ne kamar yadda yake sananne cewa kafirci matakai matakai ne.