Hanyar fassara Alkur'ani

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya saukar da littafi mabayyani ya zamo shiriya da haske ga masu takawa, kana ya zama ceto da rahama ga muminai, tsira da amincin Allah su tabbata ga cikamakin Annabawa da manzanni, wanda aka aiko shi ya zama mai bushara da gargadi ga talikai, shugabanmu kuma Annabinmu Muhammad Al Mustafa da alayensa masu shiryarwa, ma'abuta albarka, wadanda Allah ya tafiyar da dauda daga gare su, kana ya tsarkake su, tsarkakewa, da sahabbansa zababbu wadannan da suka bi shi da kyautatawa da cika alkawari har ya zuwa ranar Alkiyama.

Bukatuwa zuwa ga tafsiri

Bayan haka, hakika bukatuwa zuwa ga tafsirin Alkur'ani mai girma ba ya yankewa a dukkan zamani, domin kuwa zamani yana sabunta kansa ne, wanda hakan yana da tasiri wajen kara fahimtar Alkur'ani, tare da hadafin da yake dauke da shi mai girma:

Allah Ta'ala yana fada a cikin littafinsa mai girma cikin suratu Fusilat aya ta: 53 "da sannu za mu nuna musu ayoyinmu a sasanni (sammai da kassai) da kuma a kawunansu, har sai ya bayyana gare su cewa shi (Ubangiji) gaskiya ne..."

Domin bayyana manhaja ta tarbiyya a zamanance cikin tafsiri kana da isar da ma'anonin Alkur'ani ba tare da wahala ba, gami kuma da kokarin bayyana abin da Allah yake nufi da ayoyinsa, don haka ne

hanya da tafi dacewa wajan fassara alkur’ani tana cikin wadannan manhajoji ne :

Ta farko: Tafsirin Alkur'ani da Alkur'ani, wato fassara Alkur'ani ta hanyar amfani da ayoyin Alkur'ani.

Ta biyu: Yin tafsirin Alkur'ani ta hanyar yin amfani da sunnar Annabi (S.A.W.A.) tare da ruwayoyin da aka samo daga Imaman Ahlul Baiti (A.S.) Bisa dogaro da ruwayar nan mutawatira wacce littattafan hadisan dukkan bangarorin musulmi suke cike makil da ita, a inda Ma'aiki (S.A.W.A.) yake cewa: "Hakika ni na bar muku nauyaya guda biyu: Littafin Allah da zuri'ana 'ya'yan gidana, domin

lallai wadannan ababe biyu ba za su taba rabuwa da juna ba har sai sun iske ni a tafkina (aljanna)".

Wannan ruwayar ta zo cikin littafai da dama, ga kadan daga Idnsu:

1- Sahih Muslim babin falalar Ali bin Abi Talib

2- Musnad Ahmad bin Hanbal juzu'i na 4 shaft na 366.

3- Sahih Tirmizi juzu'i na 13 shafi na 199 babin manakibu ahlil Bait.

4- Sunanul Baihaki juzu'i na 3 shafi na 148 da kuma juzu'i na 7 shafi na 30.

5- Mustadrakus sahihain juzu'i na 3 shafi na 109.

6- Usdul Gaba juzu'i na 2 shafi na 12.

7- Hilyatul Auliya juzu'i na 1 shafi na 355.

8- Tarikhu Bagdad juzu'i na 8 shafi na 442.

9- Majma'uz zawa'id juzu'i na 9 shafi na 163.

10-Kanzul Ummal juzu'i na 1 shafi na 48.

11- As-sahawi fi mushkilil Asar juzu'i na 4 shafi na 368.

Mawallafan Tafsirin Rabi’ul Muminina sun yi nuni da mafi kyawon hanyoyi da suka yi amfani da su wajan fassara ko tarjama littafi mai girma na alkur’ani, kamar yadda suke cewa:

Hakika mun yi kokarin yin bayani dalla dalla da saukaka harshen da muka yi amfani da shi cikin wannan takaitaccen tafsirin domin isar da abin da ayoyin suka kunsa zuwa ga matasa muminai manyan gobe cikin sauki ba tare da wahala ba kamar yadda muka yi kokari gurin nesantan yin amfani da tsofaffin kalmomin Hausa masu wuyar fahimta ga matasa.

To da yake tafsirai da tarjamomin da aka yi su cikin harshen Hausa ba su iya sun magance dukkan bukatun da al'ummar musulmi ke da su a yau ba, na daga abin da ya shafi ci gaban rayuwar zamani, saboda haka ne ma za mu iske cewa masu magana da wannan harshe na Hausa ba su gushe ba suna da bukata zuwa ga sabon tafsiri na Alkur'ani wanda zai bijiro da ilimin da zai warware muhimman abubuwan da musulmi suka isa gare shi na ci gaban rayuwa a harkoki daban daban, kamar yanda wannan, matsala ta bukatuwa ga samun sabon tafsiri na Hausa wanda ya dace da zamani ta fi shafan wadanda ba su jin yaren larabci kana ba su sanin tsofaffin kalmomin Hausa • (istilahi) wadanda malamai magabata suka yi amfani da su a tafsirin Alkur'ani da tarjamarsa .

To domin sauke nauyin da muke ji ya doru a kanmu a shar'ance

dangane da al'ummarmu ta musulmi, kana saboda neman yada fahimta ta musulunci tsantsa, sai muka fara rubuta wannan takaitaccen tafsirin don sauke wannan nauyi da kuma biyan bukatun da al'ummarmu ta musulmi ke da su a wannan fage.

Kana mun ambaci wannan takaitaccen tafsirin da sunan "Rabi'ul Mu'uniinina fi tafsiril kitabil Mubin".

Ma'ana: "Dausayin muminai cikin tafsirin littafi mabayyani".

Manhajar da muka bi cikin wannan tafsirin:

Lallai mun bi hanyar fayyace ababen da suke bukatan  bayani tare da bayyana mahangar Mazhabar Ahlul Bait (A.S.) na daga ababen da suka shafi: tarihi da akida, kana da tarbiyya da wanin wadannan, kamar yanda muka yi kokarin bayyana falalar surorin Alkur'ani a farkon kowace sura bisa dogaro da hadisan da aka samo daga Annabi (S.A.W.A.) da Ahlul Baiti (A.S.).

Muna mika godiyarmu ga 'yan uwa malamai wadanda suka taimaka gurin karfafa mana gwiwa kan ci gaba da wannan aiki na tafsirin Alkur'ani mai girma, kamar yanda muke gode wa sauran 'yan uwa wadanda suka taimaka da harshensu da hannunsu gurin samar da abin da muke bukata har zuwa lokacin da wannan aiki ya kammala.

Hafizu Muhammad Sa’id Kano Nigeria.